Monday 7 August 2017

RYM 7

🤦🏾‍♀         *Rayuwar*        🤦🏾‍♀

          🙆🏾       *'Ya*    🙆🏾

🙎🏽            *Mace*              🙎🏽

Na B.A. Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*07*

Firgigit ya tashi, ba karamin bugawa zuciyarsa tayi ba ganin Rufaida tsaye a bakin kofarsa, juyawa yayi gun Nicky da tayi zuru zuru da ido ya mata wani banzan kallo sannan ya tashi dan sa kayansa ficewa Rufaida tayi idonta na zubar hawaye.

Da sauri ya gama sa kayansa ya bi bayanta, hr ya kusa kofa ya juyo yace "I always tell u to liv as early as possible amma baki ji so dnt b here wen i cm bk n kr ki sake zuwa sai na nemeki, yana ficewa itama ta tattara kayanta ta fice.

A hnkali ya turo kofarta ya shigo tareda sallama, can kan gado ya gnta rakube fuskarta na kallon gefe amma hakan bai hanashi gano hawayen da ke bin kuncinta ba, cikin sanyin jiki ya karaso ya zauna gefenta tareda kwantar da kansa a cinyarta shima ya fara kuka haka sukayi tayi hr kusan minti biyar ba wanda ya budi baki, can MK ya dago ya share hawayensa sannan ya kai hannunsa kan na yayartasa ya rike "am sorry sis, pls kar kice zaki tafi ki barni wlhy sharrin shaidan ne, i promise u wnt eva see dt again but pls dnt liv me ya fada yana hawaye, juyowa tayi ta kallesa da jajayen idanunta tace "MK tafiya dole inyi but abu daya zan gayama wannan sabon rayuwa da ka dauka ba rayuwa bace n if ka ce zaka cigaba a haka toh ka sani ka fada hanyar halaka, da kasan girman wannan zunubi da kake aikatawa da baka yi ko mafarkin aikatasa ba, ina mai baka shawara ka yarda wannan rayuwa tun wuri in kuma ka ki wlhy ba ni ba kai kuma in na sa kafa na fice a gidannan bazaka sake gani ba ko daddy sai dai muna gaisawa ta waya, indai rayuwar da ka zaba kenan toh ka sani bani ba kai mantawa zanyi inada wani kani tana gama fadin haka ta juya mai baya tayi kwanciyarta tace " ka fita bacci zanyi, cikin sanyin jiki ya fice ya bar dakin dan tunda suke bai taba ganin bacin ranta ba sai yau kuma sanin shi ya ja ba karamin damunsa yayi ba, yau ma tsautsayi ya sa ya kawo nicky gida if not can gidanta suke haduwa su gama abunda zasuyi ya dawo kuma ba wanda ya san wannan rayuwar da ya dau wa kansa. Dakinsa ya wuce ya dauki key ya fice.

Gefen gidansu Sabbura naga yayi parking ya fito ya nufi shagon da ke kallon gidansu, samarin da ke wajen suna hangoshi suka fara "MK!!!! har ya karaso basu bar ihun sunansa ba, daya daga cikinsu ne ya tashi ya ja mai kujera ya zauna tareda mika musu hannu suka gaisa, daya daga cikinsu yace " ya dai MK naganka wani sukuku haka hop lafia, ajiyar zuciya yayi sannan yace "my guy bari kawai ina cikin wata yar damuwa ne but komai wl b normal soon, miko masa taban da yake sha yayi tareda cewa "zuka daya ya isa ya tarwatsa duk wata damuwarka, dariya MK yayi tareda kawar da kansa yace " ai wannan sai ku, ka san bn wannan harkar taku,ni kunga tafiyata ma kr ku cutar da ni da hayakin sigarin naku, ya tashi yana mika musu hannu daidai lokacin Sabbura ta shigo shagon da sallamarta cikin shirinta na islamia, ko kallon gefensu batayi ba ta siya abunda zata siya ta zo zata fice ta kusa cin karo da MK da ke kokarin fita, ja da baya tayi dan ya wuce shikuwa hararanta yayi tareda jan wani tsaki sannan ya fice, tabe baki tayi dan ta ganesa kuma shima ya ganeta dukda nikabin da ke jikinta, a zuciyanta tana tunanin irin wannan halin na MK, yau dai yaci darajar shigar da ke jikinta if not da sai ta gaya mai magana dan ta tsani tsaki a rayuwarta, har ta fito bai bar wajen ba yana tsaye jikin motarsa yana waya yayinda hannunsa ke kan kofar motar, kallo daya ta mai ta kau da kai ta cigaba da tafiyarta yayinda shikuwa yabi bayanta da kallo yana mamakinta ace mutum kullum kana wani lullube kanka, sai da ya daina ganinta ya shige motarsa yana mamakin tsayawa da ya yi yana kallonta.

*WANENE MK*?

*Muhammad Kabir Mansur* shine asalin sunansa  'da na biyu ga Alhaji Mansur Bilyamin, kyakkyawa ne ajin farko yanada tsayi sosai ga kuma haske da Allah ya mishi wane balarabe, su biyu iyayensu suka haifa shida Yarsa Rufaida, bayan su iyayensu ba su sake haifuwa ba, aiki ya kai Abbansu Korea inda suma a can suka yi yawancin rayuwarsu dan MK ma a can aka haifesa.

MK na da shekara goma mahaifiyarsu ta bar gidan, haka kawai suka wayi gari suka ga bata nan, dalilin haka Abbansu ya tattarosu suka dawo gida Nigeria.

Rufaida da MK sunyi kuka sun gaji tunba MK ba dan ba karamin sabo yayi da mahaifiyar tasa ba dan har rikesa a asibiti sai da aka yi da kyar aka samu aka shawo kansa ya dawo normal amma ynxu ko maganan ummansa bai so a masa dan duk sai yaji ya tsaneta . Gatansa sune Rufaida da Daddy sai kuma Nani da tun zuwansu Nigeria take taredasu tun MK ba ya sonta hr suka saba inda yanzu yake jinta tamkar mahaifiyarsa, kuma itama tana sonsu tamkar 'yayanta shi yasa Rufaida ke wa Daddynsu sha'awar aurenta.



Zaune suke a dakin Anna, hira suke bnda sabbura da ke gefe tanaiwa kannenta bitar karatu, sallamar wani almajirine ya katsesu yace "wai ana sallama da Sabbura, ko dagowa batayi ba balle ta yi yunkurin tankawa, Shamsiyya ce tace "kace tana zuwa sannan ta dubi inda Sabbura take ta mata ido, sai da ta dan bata lokaci sannan ta tashi ta fice yayinda Shamsiyya ta bi bayanta suna fita Anty Suwaiba ta juyo gun Anna tun kan ta ce wani abu Anna ta daga mata hannu tace " Suby mun gama maganan nan kuma kin nuna mun baza sake dagota ba sabida haka bn son jin komai, cikin sanyin jiki tace "toh Anna bazan sake magana akan wannan batu ba, amma zuciyanta cike yake da haushin kannen nata.

Sabbura na shiga dakinsu shamsiyya ta shigo itama, ita ta tayata shiryawa hrda mata yar kwalliya duk da Sabbura bata so hakan ba, fesheta da turare tayi ta rakota hr bakin kofa sannan ta koma.

Can gefe ta hango shafiq na tsaye jikin motarsa, karasawa tayi cikin takunta a hnkali, shi kuwa tunda ya hangota ya kasa dauke idonsa, komai nata burgesa yake, yanayin tafiyarta ma abun kallone, hr ta karaso bai dauke idonsa a kanta ba, sallama ta mai ya amsa sannan suka dan gaisa tace mai su shiga daga ciki.

Side na Abbanta suka nufa dan dama yace duk sanda ya zo suna zuwa side nasa, kujeru ta aje musu sannan ta tashi ta dauko mai ragowar kunun aya da tayi yana sha suna hiransu, da ya tashi tafia har wajen motarsa ya sa ta rakasa inda ya miko mata wani leda, kin karba tayi, ba ynda beyi da ita ba amma sam taki karba, ya dubeta yace " nasan zakice its too early but ni a wajena hakan ba komai bane, wayace dama na siya miki sabida in nazo ba sai na aiki yaro ba kuma duk sanda wata bukatar yin magana dake ya taso zn kira musamman in nayi kewarki kema kuma zaki iya kirana, duk wata bukata naki da ya tashi zaki iya nemana a waya ni mai yi mikine Abba da kansa ya bn go ahead so bn ga dalilin da zaki ki krban kyautan da ur husby to be ya miki ba, murmushi tayi sannan tace " nagode sosai da wannan kyautar taka amma a gaskia bazan iya karban wannan kyautar taka ba, dalilin kuma bazan iya fadama ba, in gaisawa ce duk sanda naji bukatar hakan zan karbi wayan addana in kiraka da shi amma kayi hakuri dan wannan kyautar ta mun girma.

Ajiyar zuciya yayi yace "toh shikenan, nasan tunda kika ki karba dalilinki zai zamto mai karfi sabida haka bazan tilastaki akan ki karba ba sai dai zan cigaba da aje miki shi har zuwa ranar da zaki bukata. Hango Abbanta da tayi shiyasa ta mai sallama ta shige gida shi kuwa ya tsaya ya jira ya karaso suka gaisa.

Dakin Anna ta wuce ta tarar kannen nata hr sunyi bacci ta dagasu ta gyara musu kwanciyarsu sannan ta hau tattara takaddunsu. Abbane yayi sallama ya shigo dakin duk suka amsa mai, inda Sabbura ke zaune ya nufa ya aje mata wani leda sannan ya juyo yace "Sabbura ga sako ance in kawo miki, yana gama fadin haka ya fice, yana fita Shamsiyya ta zo ta ja ledar dan Sabbura ko kallon ledar batayi ba, ihun da Shamsiyya tayi ya ja hankalin kowa a dakin, rungume Sabbura tayi tana " wow sis am so happy for u, wayace sabo gal kirar Tecno case da aka sawa wayarma kadai abun kallone balle ita wayar kanta, mika mata wayar shamsiyya tayi bata ma yi yunkurin kaima ummarta ba dan tasan mai zai biyo baya, sauran yayyunta kawai  ta nuna wa wayar, anty suwaiba ne ta krbi wayan tana duddubawa tace "Iye irin waya tacema saura kuma ynxu anga ana rike irin wayata a dauka level daya muke, dole ma incanza wayane kawai dan bazai yu ki rike irin wayar dake hannuna ba, warce wayan shamsiyya tayi tace " a tsufar lafiya will hv bn k, bawai a tsaya ayita  maganar da bashi da amfani ba, tashi tayi Anna ta jawota ta zauna tace "Anna da kin bari na jima yarinyarnan ciwo dan sam batada kunya wlh ki ka mun iskanci daddakaki znyi kuma gobe in hanaki binmu abujan, yar gajeriyar dariya shamsiyya tayi tace " in ur dreams kenan, tattara ledan tayi ta ja Sabbura suka br dakin.

A daren ta gama koyawa Sabbura abubuwan kan wayar dan tasan bata iya komai ba, har su watsapp ta bude mata ta koya mata ynda ake chatting sannan shamsiyya ta kwanta ta brta sabida tafiyar da ke gabansu.



Shakuwace sosai ynxu tsakanin Sabbura da Shafiq inda suketa zuba soyayyarsu mai tsafta har manya ma na kokarin shiga ciki Abbansa kawai ake jira ya dawo daga course da yaje a kasar waje a turo. Ba karamin dadi Sabbura taji ba dan ko ba komai zata huta da wahalar gidansu.

~~~~

Rufaida ce zaune a dakinta tana nazarin wani littafi,rufewa naga tayi ta tashi ta fice daga dakin. Hanyar dakin M.K ta nufa dan tun sanda ta kamasa da nicky ba su sake haduwa ba dan kulle kansa yake a daki bai ko fita, a hankali ta tura kofar dakinsa ta gansa zaune ya kurawa wani frame ido bai ma san da shigowarta ba hr ta zo ta zauna ta sa hannu ta krbi frame in taga hoton ummarsu, juyowa yayi yana ganinta yayi yunkurin tashi, kamo hannunsa tayi ta maida shi sannan ta juyo da fuskarsa taga idanunsa sunyi ja ga dukkan alamu kuka yayi, riko hannunsa tayi tace "I knw u miss her, we ol do, cire hannunsa yayi daga nata cikin bacin rai yace " I hate her, n u dnt miss ppl u hate n pls lts not talk abt dis cos u knw how i react abt dat more dan anyone so pls lets not start, jan bakinta tayi tayi shiru har kusan minti uku bawanda ya sake magana sai can ya juyo yace "Yaushe tafiyarki?
" Gobe insha Allah ta bashi amsa, "So u r really going? Kai kawai ta gyada mai, " even after i promised u dt i wil change? Riko hannunsa tayi tace "M.K, i knw u, n lyf da ka dauka its not u n nasan zaka bari, me staying wunt change a thing, kai ba yaro bane u knw wts ryt n wts wrong ba sai an gayama ba if u r rily willing to change u"ll change, n i promise i wil come visit any chance i gt ok", cire hannunsa yayi daga nata bai ko sake kallonta ba ya tashi ya shige toilet, tashi tayi itama ta fita dan tasan ynxu kam ba abunda zata gaya mai yaji.



Cikin shiri Rufaida ta fito da yar trolleynta ta wuce dakin Abbanta, ta jima a ciki sannan suka fito inda shi yayi kasa ita kuwa tayi dakin M.K ta jima tana knocking amma yaki ya bude, wayanta ta ciro ta kirasa tana ji yana ringing amma yaki picking, wucewa kasa tayi kawai inda Abba ke jiranta.

Gefensa taje ta tsaya, dan rungomota yayi ta gefe yans patting nata yace " Yaki saukowa ko, dnt u worry jst gv him time, dagowa tayi tana mai murmushi sannan ta basa hug tace "I will miss u so much Dad n pls batun Nani i hope to hear good news soon, murmushi yayi sannan yace " I will miss u too my princess, n u"ll hear good news cos i will do evrytn dt mks u hapi.

Nani ce ta fito daga side nata ta nufosu, gaisawa sukayi duka sannan ta karbi akwatin Rufaida sukayi waje duka, har wajen driver suka rakota rungume Nani Rufaida tayi tareda cewa ta cigaba da kula da M.K dan ynxu he nids her more dn eva. Sai da sukaga ta fice sannan suka koma cikin gida.

Rufaida na shiga airport ta je ta gama abunda zatayi ta je ta zauna tana jiran a kirasu, bai jima ba kuwa aka kirasu ta tashi ta yi hanyar da zai sadata da inda zata hau jirginsu, juyowa tayi dan taga ko zata hango MK dan duk a tunaninta bazai bari ta tafi basuyi sallama, ganin ba ko alamunsa ya sa ta cigaba da tafia, hr ta sa kai ta sake juyowa ta hango MK ya shigo cikin sauri-sauri gudu-gudu, suna hada ido ya tsaya yana hucin gajia, juyawa tayi taje ta karasa inda yake ta riko hannunsa ta nema musu waje suka zauna, zuwa akayi aka mata magana akan cewa in ta bata lokaci zatayi missing flight nata juyowa Rufaida tayi ta ce ba matsala zata kama next one in.

Kusan minti biyar suka dauka suna zaune sannan MK ya juyo yace "am sorry sis for d way i acted, its very selfish of me a ce in hanaki tafia, i knw in ba dole ba u wunt liv me here am really sorry for trying to stop u frm living, share mai hawayensa tayi tana rarrashinsa har yayi shiru, hira sukayi hr aka sake kiran jirginsu sannan suka rabu yana daga mats hannu hr ya daina ganinta.

Cikin sauri ya bar airport in ya je ya shiga motarsa ya hada kansa da steering ya hau kuka, tunda yake da 'Yarsa bai taba yin nisa da ita ba kuma sun saba sosai shi yasa ynxu duk ya damu, sai da ya sha kukansa sannan ya sa wa motar key ya figeta cikin zafin nama.

Sabbura ta taso daga gidansu Atika kenan tazo daidai gidan nicky ta ga motan MK yazo yayi parking daidai kofar har ya so ya bugeta, tana ganinsa ya fito ya hau buga kofar gidan, batayi mamaki ba dan dama shi bai yi kama da mai hankali ba sai dai batasan rashin hankalin ya kai haka ba, rage tafiyarta tayi dan ganin ikon Allah dan tasan wacece Nicky kusan duk anguwama an santa, gogaggiyar karuwace kuma duk mai shiga gidanta toh ba mutumin arziki bane, gani tayi an bude kofar nicky ta gani daga ita sai wata yar vest sai yar guntun skirt da bai kai gwiwa ba, ganin nicky na kallon gefe ya sa MK juyowa ya ga Sabbura da ta tsaya ta kasa motsi kasa dauke idonsu sukayi duka har sai da nicky ta kama hannunsa ta shigar da shi tareda watsowa Sabbura harara sannan ta rufo kofar.

Sabbura kuwa mamakin knta ta fara ganin ta tsaya kallon abunda bai shafeta ba,gyara daurin nikabinta tayi sannan ta wuce gida.

Share:

0 comments:

Post a Comment

Blog Archive

Search This Blog

Contact Form

Name

Email *

Message *