Thursday 10 August 2017

RYM 12

         Rayuwar      

              'Ya

           Mace           

Na Billy Ladan

*EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*12*

bintladan.blogspot.com

_Wannan shafin nakune,kungiyata abun alfaharina *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* U guys r lyk family, I heart u ol_

Marin da Sabbura ta sauke wa MK shi ya jawo hankulan mutane, kan kace meh an taru a gefensu, nunosa tayi da yatsa tace "ga ka babban  mahaukaci, maras tarbiya wanda baisan mutuncin nagaba da shi ba, ai a haife wannan bawan Allah ya isa yayi jika da kai amma dan rashin 'da'a ka daga hannu ka sharara mai mari, uban meh kake takama da shi,kudi ko meh? Wlhy ka canza kidi dan rawarka ta sauya dan wannan ba dabi'a bace in kana yi a wani waje ana kyaleka toh irinmu baxa mu gani mu kyale ba kuma ka bi dunia a hankali dan gaba baka san da wa zaka hadu ba.

Mayar da hankalinta gun tsohon tayi da haryanxu yana rike da kumatunsa tace " Baba ina zaka yine? "Gomari zani ya bata amsa, tace " toh muje Baba in saka a mota, riko sandarsa tayi dan yi mai jagora, ya juyo gun MK da kunya ta gama lullubesa ganin yawan mutanen da ke wajen ciki harda boys nasa yace " 'dana duniyace, ta ishi kowa darasi in kayi mai kyau dan kanka in kuma kayi akasin haka duk wa kanka kuma ka guji bakin manya dan tamkar guba take a gareku yara, ya juyo gun Sabbura yace "ke kuma yata Allah ya miki albarka, Allah yasa ki gama da dunia lafia, Allah ya baki miji nagari da 'ya'ya ma su jin kanki, " amin" ta amsa mai tana mai jin dadin addu'arsa sannan ta wuce ta sashi a napep ta ciro naira hamsin da ta mallaka ta bawa mai napep in yayinda tsohon ke ta sa mata albarka.

Bata ko dubi inda MK yake ba tayi sauri ta shiga kwanar gidansu Atika, tana shiga soron gidan ta sunkuya tareda rike xuciyanta numfasinta sai fita yake da sauri sauri, mamakin kanta take da har ta iya marin MK tareda gaya mai maganganu son ranta abunda bata taba yi ba amma ko ba komai yau ta huce haushi tunda ta rama abunda yake mata.

MK kuwa mutuwar tsaye yayi a wajen, maganganunta bai bata mai rai kamar marin da ta mai ba, lalle kuwa yarinyar nan ta jawa kanta bala'i ya fada cikin ransa, juyawa yayi gun mutanen da suka tsaya suna kallonsa ya daka musu tsawa duk suka watse, abokansa ne suka karaso wajensa shima harara ya bisu da shi suna mai magana yayi banza da su ya shiga motarsa ya figeta cikin zafin nama, bai tsaya a ko ina ba sai gidan Nicky.

Falonta ya shiga ya zauna bai ma sanar da ita shigowansa ba, jinginar da kansa yayi a jikin kujerar yayinda ya daura kafa daya kan daya, daya kafar sai jijjigata yake, rufe idonsa yayi yayinda yake gano kwayar idonta lokacin da ta maresa ta kuma tsaya ta gaya mai magana son ranta, bude idonsa yayi naga har sun canza kala sunyi ja cikin bacin rai ya dunkule hannunsa ya kai wa center table da ke gabansa naushi wanda hakan yayi sanadiyar fashewarsa da yankewar hannunsa amma sam bai damu ba, jin karar ya sa Nicky fitowa cikin shirinta dan dama ta shirya, jiransa kawai take yazo su fita.

Ganin abunda ya faru ya sata karasowa da sauri ta rikosa tana "MK wts wrong? Jawota yayi ta fada jikinsa ya fara kissing nata dan shine kadai abunda yake ji zai kwantar mai da hankali ya dauke mai tunanin wancan aljanar. Da kyar Nicky ta kwaci kanta daga jikinsa ta riko hannunsa ta ce "MK u r bleeding ka tashi muje asibiti, tsaki yayi yayinda ya tashi ya wuce dakinta, binsa tayi itama ta bude drawernta ta ciro wani dankwalinta ta zo ta zauna gefensa ta dago hannun da ke ta zubar da jini ta daure mai ta gama ta juyo taga har yayi bacci tashi tayi ta cire kayanta ta sa na shan iska ta haye gado, ji tayi ya fara magana cikin bacci yana cewa " ku tabbatar kowaye ita kun kamota kun kawo mun ita a daren nan nake son ganinta in ba haka ba ranku zaiyi mugun baci, bugesa ta danyi sai gashi ya farka dan dama baiyi nisa ba, rai a bace tace "wa kake cewa za a kawo ma a bacci?, so duk abunda nake ma bai isheka ba kana neman wata MK toh wlhy baka isa ba, i gv u everything, jst bcs of u na daina kula kowa sai kai i was willing to gv everything up just to b with u but u nva sim to notice ba ka daukeni a matsayin komai ba sai wanda zaka huta da ita kawai n i wunt tk dt cos i want more n baka isa ka kula wata ba in as much as ina raye, tsaki yayi tareda tashi ya zauna yana mata kallon raini yace " i hv no idea maganar meh kike, in ma wani abun kika ji toh ki tattara ki zubar dan ni MK mata basu gabana dats y kika ga har yau bnyi aure ba kuma bnda ra'ayin yi kuma ds shld b d last tym da ina bacci zaki tasheni kuma ki sani ba ke kadai zan iya kai wa matsalata ta biya mun bukata ba so dnt lt ur hopes up in ma gani kike zan aureki o sumtn lyk dt gwara ki aje gefe in kuma dts wt u r after zn iya barinki in nemi wanda bazata na tayar mun da hankali ba, matsowa tayi da sauri ta riko hannunsa tace "am sorry dear bazan sake maganar ba dan Nicky na bala'in son MK kuma bata jin zata iya rabuwa da shi, kawar da kansa yayi ta kamo fuskansa ta juyo, ganin hannun mutum kwance a fuskansa ya sata shafa wajen cikin nuna kulawa tace " My luv wa ya mareka a nan? janye jikinsa yayi tareda sauka a kan gadon, gaban mirrornta ya nufa ya tsaya yana duba fuskarsa sai yanzu yaga hannun Sabbura kwance a fuskansa, hannunsa mai ciwon ya daga ya naushi jikin drawernta da shi, azabar da ya ziyarceshi shi ya sa shi yin baya tareda riko hannunsa, da sauri Nicky ta sauko ta karasa inda yake dunkule a kasa tana mai sannu, tashi yayi ya ja shirt nasa ya fice batareda ya ce da ita komai ba.

Da kyar ya iya driving kansa ya iso gida yana shiga gida bai yarda ya hadu da kowa ba ya shige dakinsa,toilet ya fada ya sake wa kansa shower, hannu ya sa ya shafi  inda Sabbura ta maresa sannan ya kai dubansa ga hannunsa da har yanzu yake fitar da jini kadan kadan yace "kamar yadda a dalilinki na samu wannan tabo toh wlhy kema sai na miki tabon da har ki mutu baza ki iya gogewa ba. Hannunsa na zafi haka ya daure ya wanke wajen ya fito ya shirya ya wuce aid box nasu yayi dressing sannan ya koma sama, yinin ranar a daki yayi dan baya so iyayensa su ga fuskansa.

Har bacci ya fara daukansa yaji bugun kofarsa ya taso ya bude, ganin boys nasa ya sa ya mayar da kofar zai rufe amma suka rike suna haba MK ka sauraremu mana, bude kofar yayi tareda yin gefe dan su shige suna gama shiga ya rufo kofarsa ya koma kan gadonsa, ganin hannun Sabbura kwance kan fuskarsa ya sa su fashewa da dariya wanda hakan ya dada kular da MK yayinda yake kara jin tsanar Sabbura a ransa dan ko ba komai ta gama zubar dashi a gaban boys nasa, juya musu baya yayi yace " in kun gama dariyarku zaku iya fita, shiru sukayi sannan babbansu yace "Wlhy MK Sabbura tayi da kai amma ba laifinta bane ba ta san ko kai waye bane shi yasa, juyowa yayi yana mai maimaita sunan " Sabbura" kai ya daga mai yace dts her name, dariyane ya kubce wa MK, ganin yana dariya suma suka biye mai, da kyar ya iya tsaida dariyarsa yace "wannan wani irin suna ne, sai kace yar tsintuwa, " inaga sunan larabcine" dayan ya bashi ansa, dariya MK ya cigaba dayi yace "duk da ba larabcin nake ji ba i doubt if sunan larabcine wannan ya karashe yana dariya, but anyways ko ma me take da suna zata gane kuranta zata san ta tabo MK zata kuma san ba a mun in bari, kuma bana barinta ta kwana sabida haka inaso in baku wani aiki, tashi yayi ya bude drowernsa ya ciro wani akwati ya zo ya aje a gabansu ya bude, ganin yawan kudin da yake ciki sai da duk suka razana, murmushin mugunta yayi sannan yace " ku dauka kuje zan turo muku da text in abunda nakeso kuyi da kuma inda zaku sameni bayan kun gama, hannu na rawa suka dauki akwatin tareda sara mai babbansu yace "muna jira oganmu, hannu kawai ya daga musu sukayi waje. Suna fita shima ya dauki key ya fice ya bar gidan.

Ayi hakuri da wannan

Billy Ladan ce

Share:

0 comments:

Post a Comment

Blog Archive

Search This Blog

Contact Form

Name

Email *

Message *