Sunday 6 August 2017

Rayuwar Ya Mace

🤦🏾‍♀         *Rayuwar*        🤦🏾‍♀

          🙆🏾       *'Ya*    🙆🏾

🙎🏽            *Mace*              🙎🏽

Na B.A.Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*01*

Zaune take akan sallaya tana lazimi tana jira a kira assalatu dan ta tashi ta gabatar da sallar asuba, tana zaunen har aka kira sai da taji masallatai sun fara sallah sannnan itama ta tashi ta gabatar da sallanta. Jingina kanta tayi da bango dan ta dan huta kafun ta kama aiki, kaman daga sama taji aka fara kiranta "Sabbura! " Sabbura!!
A hankali ta tashi ta nade sallayan ta dubi Anna da ke zaune tana nazirin wani takadda ta ce "Anna ina kwana? Wanda ta kira da Anna ko dagowa batayi ba sai ma dai ta cigaba da abunda take, fita tayi dan inda sabo ta saba da wannan hali na mahaifiyar tata.

Tana fita ta ci karo da Baba saude fuskan nan murtuk ba ko alamun daria, a hankali sabbura ta karasa ta dan russuna tace " Baba Saude ina kwana? Bugu ta kai mata tana "Munafuka in ban kwana ba kya ganni a nan, shegiyar ya da naketa ihu dama kina ina?, sunkui da kai tayi tana rikeda kanta inda Baba saude ta buge, a hankali tace "Baba Saude Sallah fa nake, " Toh sallau kullum aka taboki sallah sai kace kinfi kowa ibada anjima kuma kice zaki dauki tsirarun kafarki kice zaki makaranta toh wallahi idan kinga kin fita a gidannan kin gama ayyukanki ne gaba daya, ban damu ko zaki latti ba sabida haka yi maza ki kama aiki, Komawa daki Baba Saude tayi yayinda Sabbura ta wuce ta hura wuta, shayi ta fara daurawa sannan ta debo tulin dankalin hausawa ta fara ferewa.

Abbanta ne ya shigo dawowarsa daga masallaci knan ya ganta tana aiki kai kawai ya kada sannan ya karaso inda take, tana jin kafar mutum ta juyo tana ganin Abbantane ta dan sauko daga kan kujerar da take tace "Abba ina kwana?  " lafia lau sabbura ya amsa mata sannan yace "har kin hau aiki, toh ina sauran yan uwan naki? " basu tashi ba Abba ta basa amsa, "maza je ki tada su dan wannan aikin ya miki yawa, " Abba ba sai an tadasu bama ai ba yawa ynxu zn gama.

"Ki dai tadasu Sabbura cewar abbanta, " a'a Abba wlhy abarsu zan gama ai na saba, "toh shikenan Sabbura dan ya san abunda take gudu yace " Allah ya miki albarka Sabbura, ki cigaba da hakuri wataran zaki ci moriyarsa, "Amin baba nagode ta amsa mai  ya tashi ya shige zuciyansa cike da tausayin yar tasa.

Tea na tafasa ta dauki flask ta sa wa kowa nasa sannan ta soma soya dankalin bai dau lokaci ba tagama tayi sauce sannan ta daura ruwan wanka dan lokacin sanyine sannan ta fara share cikin gidan tas ta hado wanke wanke tayi, kafun ta gama har ruwan yayi ta sauke sannan ta shige dakin Anna cikin sauri ta gyara ta sa turare ta fice dan tada kannenta, sai da ta musu wanka sannan itama ta yi ta shiryasu gaba daya ta samu musu breakfast nasu a cooler dan sun so suyi latti, dakin Anna suka shige kannanta Shahid da Sameera suka gaida Anna ta amsa musu cikin sakin fuska sannan ta ja purse nata ta ciro hundred naira guda biyu ta basu, Samira sarkin baki tace " Anna na Anty Sabbura fa? Ko kulata Anna bata yi ba ganin zata dameta yasa ta daka mata tsawa tace " zaki fara shegen nacin maganartaki ko, in baki bace mun a nan ba kema sai in karbe kudin nawa, yi tayi kaman zatayi kuka tazo ta fada jikin yayar tata, Sabbura ta dagota tana rarrashinta ta kamo hannun Shafiq suka fice.

Tana sa kafarta cikin tsakar gidan ta hango Baba Saude zaune bakin kofarta tana ganinta tace "Wannan 'ya da bakin hali kike, ynxu abincin ma sai mun biyo mun dauka toh maza sake hannun yarannan ki kai musu abinci kuma ki jirasu su gama kan ku wuce, in ba bakin hali da mugunta irin taki ba meh ya hanaki kai musu abincin, ba tareda ta sake hannun kannen nata ba tace "Baba Saude wlhy mantawa nayi kuma ai inba yau ba bn taba fashin shigarwa ciki ba, tunda yau basu gani ba ai kamata yayi su fito su dauka, Salati Baba saude tayi tana tafa hannu tace " Oh ni Saude, Sabbura har kinyi girman da ina fada kina fada toh wlhy maza kizo ki kai musu abincin nan kuma kafarki kafarsu in yaso duk kuyi lettin a taru a daka ai dama can muguntarki yasa kikayi hakan dan a jibga mun 'ya'ya ko? Toh wlhy sai dai a hada dake, "Yi hakuri Baba saude cewar Sabbura, wlhy ba da gangan nayi ba amma gaskia sai dai su fito su dauki abincinsu kuma ni baxan iya jiransu ba dan sai na biya na ajesu sameera zan wuce, Tashi Baba Saude tayi tayo kan Sabbura ta fara ja da baya dan ta san meh hakan ke nufi, jiyo Muryan Abbanta tayi yace "ke Sabbura ba makaranta zakuje ba zo maza ku wuce, Godia tayi wa Allah a ranta da ya kawo abbanta sannan ta bi gefen Baba Saude da take hararanta tana mata kallon zaki dawo ki sameni ne ta fice, har ta kai kofa Abbanta ya kirata ta ja ta tsaya tareda juyowa, karasowa yayi ya bude zip na jakarta ya sa mata abu a ciki sannan ya rufe ya musu addu'a sannan suka fice. Tabe baki Baba Saude tayi ta shige daki

Napep ta tara musu suka shiga sai da ta aje su itama ta yi hanyar ajinsu, dakali ta nema ta zauna dan ta kagu ta ga meh Abbanta ya sa mata a jakar, tana budewa taga yar tsohuwar dari biyu take taji hawaye ya fara zuba mata ta kankame jikinta ta zauna tana ta sharban kuka yayinda take jin son mahaifinta nata sosai tareda jin tausayin kanta, dama bata san ya zatayi ba dan dama ko kudin ruwa bata da shi ga dankali da shegen kwaran mutum dole sai da ruwa. A duk lokacin da tuno da rashin sa'arta a rayuwa ta kanji dunia ya mata baki, kukan ne kawai ke sa ta danji sauki shi yasa ta zauna take kukarta.
Ace wanda ta tsuguna ta haifeka take nuna ma tsananin kiyayya da tsana mai yafi wannan rashin sa'a a dunia, tana cikin kuka taji ance "Dan Allah ina tambaya mana, dagowa tayi ta watso mai idanunta masu fisgar hankali da sukayi ja sabida kuka, suna hada ido ta kawar da kanta, ynda ya ganta ya sashi yace " sorry i cn jst ask sum1, share hawayen nata tayi tace "no ina jinka, saurayin yace " dama office na principal naku nake nema, come with me tace dashi yana kan hanyata ta zuwa aji zan iya nuna ma, suka jera suna tafia kowa da abunda ke yawo zuciyarsa har suka iso office in ta dubesa tace "gashinan, batareda ta jira ya ma mata godia ba ta bar wajen dan zuwa aji, bayanta ya bi da kallo yana tunanin ko meke damunta haka kawai yaji yana son sanin danuwarta dan ya share mata hawayenta gashi ko tsayawa batayi ba balle ya tambayi sunanta, yana tsaye a wajen hr ta bace mai, ji yayi an dafasa ance " Shafiq har ka iso, juyowa yayi yace "eh uncle ynxu zuwana, mu shiga daga ciki toh cewar uncle in nasa sannan ya bude musu office in suka shige.






*02*

*Sabbura* *Idris* *Liman* shine asalin sunarta
Ya ta hudu a wajen Alhaji Idris Liman.
Su shida Anna ta haifa, Saliha, Suwaiba, Shamsiyya, Sabbura, Shahid sai Autarsu Samira yayinda Kishiyar Anna Saude keda yara hudu
Rahama, Rayyan, Rabi'u sai Nawar.

Iyayensu haifaffun yan Maidugurine anan jihar Borno kuma suma duk anan aka haifesu.

Alhaji Idris karamin dan kasuwane inda yake da shagonsa a nan monday market duk da ba wani karfi yakeda ba yana iya kokarinsa wajen ya kyautatawa iyalansa kuma ya sa yaransa a makaranta amma duk wannan bai hana Baba Saude surutu a koda yaushe ba dan ita haka Allah yayita bata da godiyar Allah, gata mafadaciya da wuya a wayi gari bata samun abun fada dadin dadawa kuma ita kullum a gida take sabanin Anna da ke koyarwa a wata secondary school dan dama ita da iliminta ya aurota kuma da ba dun kaddara ba da ba abunda zai sa ya auro Baba Saude dan Anna mace ce mai hankali, wanda ta san ya kamata matsalar shi daya da ita wannan *Karan* *Tsana* da ta daura wa yar ta Sabburah



♨♨♨♨♨♨♨♨

Kamar Kullum ta tashi ta gama ayyukanta dan yau tana da islamiya. Bakwai daidai  ta gama ta fito cikin shiri, doguwar hijabi ce purple har kasa sai safar hannu da na kafa da ta sa sai kuma nikabinta da ta riko a hannu, tana daura niqabin Baba Saude ta dago labulen dakinta tana mata wani kallo ita kuwa Sabburah bata ma lura da ita ba, tana juyowa ta ganta tsaye ta dan russuna tace "Baba Saude ina kwana? rike gaisuwar ki bata wannan nake ba cewar Baba Saude, da kike shirin fitan wa zaiyi karin kumallo? " Ai na gama komai Baba Saude Sabbura ta bata amsa ta kara dacewa "Har miyan rana nayi in na dawo kawai shinkafa zan daura, hakan ba karamin kular da Baba Saude yayi ba dan ita burinta a kullum tana musguna mata, nan ta fara tunanin aikin da zata sata kawai dan ta sa tayi latti dan tasan hukuncin hakan dukane, har Sabbura tayi gaba ta fara tafia Baba Saude ta ce " Toh sarauniyar sauri ai ban gama ba, ina yau mukayi dake zaki wanke mun ban daki da safe, ajiyar zucia Sabbura tayi dan ta san nufin Baba Saude kan ma ta tanka Abbanta ya sako kai tana ganinsa ta saki murmushi a zuciyanta tace "Here cums ma  saviour, kallonta yayi yace Wuce ki tafi bata ko kalli gefen Baba Saude ba ta fice cikin sauri. Baba Saude ta hau surfa bala'i " Ai dama Malam kai kake sa yaran nan su rainani in bahaka ba taya za'ace zan sa Sabbura aiki ka wani ce ta fice ta tafi ai duk wannan ni kake janyowa raini, kada kai yayi sannan yace "Saude taya yarinya ta shirya zata makaranta ki tsuro mata da aiki, aikin ma da kikasan bata karewa da wuri bace kina tausayawa yarinyan nan wlhy ina guje miki ranar da hakkinta zai biki, kyautatawar da take miki 'yayanki ma basu miki amma sam baki sassauta mata kullum burinki ki musguna mata, taresa tayi tace " Kaga Mallam ya isa, dama ba isa a tabo yar gaban goshinka ba sai ka kama wa mutum wa'azi ai tunda ka hanata yi mun aikin shikenan ai, ynxu fisabilillahi ina zan je in bukatata ya tashi , Yace "Ai ga Rahama ita meh zai hana ta wanke miki ban dakin, wani kallo ta mai sannan tace " Alhaji kai ma dai fada kake,Rahaman nawa take, zan dai jira Sabburan, kada kansa yayi yace " ai ice tun yana karami ake tankwarasa, duk abunda Sabbura zatayi Rahama zatayi tunda shekara ta bata, da a ce kina koya mata ai da tuni ta iya,tunda kin zabi jiran nata ai sai ki jira,yana kaiwa nan ya juya ya shige dakinsa yayinda Baba Saude ta bisa da harara tana "Munafakin maza kawai, ai da yar gaban goshinne da yayanta ko muryarka ba za a ji ba, inga mai hanani sa wannan shashashar aiki.




Sabbura kuwa tana fita ta wuce gidan kawarta Atika, a falo ta samesu itada ummarta suna karyawa a plate daya, zama tayi tareda gaida ummar Atika ta zauna tana jiranta ta gama su tafi, kura musu ido tayi tana sha'awar yanda suke cin abinci tare har da yar hiransu da dariya, hawaye ta ji ya taru a idanunta dan tasan wannan wani abu ne da bazata taba samu ba dan ko wuri daya basu zama da mahaifiyarta balle har hira ya shiga, kauda kanta tayi ta dan share kwallar da ya zubo mata.

Ba karamin bata musu lokaci Atika tayi ba dan sa hijabi kadai ma ta bata lokaci, suna isa kuwa sukaga an fara taran letti, Sabbura ta zaro ido dan ko kadan bata son abunda zai taba wannar farir fatarta tata mai shegen laushi dan abu kadan sai kaga jikinta ya pashe dan ko wanki mai yawa in tayi zakaga hannunta ya tsatsage.

Cikin tsoro suka karasa Atika ta mika hannunta aka bata bulala biyar Sabbura da ke gefe kuwa sai tsalle take tun kan ma a zo kanta, taki sam ta mika hannunta har Atika ta gaji ta shige ta barta, malaminsu kuwa yace ba yanda za a yi ta shiga bai daketa ba, hakan yasa ta ja gefe ta zauna tana kuka tana rokonsa.

Wata motace ta zo tayi parking a gefenta, tana ji aka fito tareda rufe motar ya zo dab inda take zaune taji ance "Malam ya ita wannan bata shiga ba take zaune a kai, " wlhy Malam Shafiq letti tayi kuma taki miko hannu a daketa shine nace ta zauna ta tayani hira dan bazan daki saura in barta ba cewar malaminsu, wanda aka kira da Shafiq yace " Hakane Mallam kayi gaskia sannan ya dubi inda Sabbura take yace "malama kalli nan, ya sunanki? Ta dago tareda cewa " Sabbura, tayi saurin ganesa as saurayin da suka hadu a school yayinda shi kuwa yake tunanin ina ya taba jin muryannan dan niqab da ke fuskarta ya hanashi ganin komai nata ji tayi yace "taso ki biyoni, cikin rawar jiki ta tashi ta bi bayansa suna shiga ya dubeta yace " ki wuce aji amma nan gaba ki kula, godia ta mai sannan ta wuce aji,

Tana shiga ta hango Atika sai dariya take mata maimakon ta je wajenta sai ta nemi wani waje ta zauna, Atiqa na ganin haka ta taso tazo ta zauna gefenta tace "Haba kawata ta kaina fushi ake danine, harara Sabbura ta mata tace Atika in na sake biya miki ki canzan suna ai da ba dan keba da bnyi latti ba amma daga yau ta kare kowa yake zuwa shi daya, nan Atika ta hau bata hakuri amma ko ta kulata dan ta gama kular da ita, matsowa Atika tayi ta fada mata abu a hankali naga ta yi daria tareda dan tureta tace " Ni barni Atiqa ban son ji muraja'a zanyi, sake matsowa tayi ta mata magana a kunne wanda ya kawo barkewan hira tsakaninsu har basu san lokacin da malami ya shiga har yayi rubutu kan allo ba, Sabbura sai zuba take, jin ajin yayi tsit ya sa su juyowa sukaga duk su ake kallo hr Malamin cikin sauri ta sauke niqabinta dan shigowarta aji ta daga yayinda ta tashi tana bawa malamin hakuri, shi kuwa zuciyansa fal murna dan ya hadu da wanda ta hana zuciyarsa sukuni, cikin sakin fuska yace "ki zauna in an tashi ki sameni a office in malamai, amma inaso ku kula aji musamman ta islamia ba wajen hira bane idan malami bai shigo aji ba sai kuyi muraja'a bawai a kafa majalisar hira ba ko a tsaya chatting da ture turen abu a waya sabida haka ku kula. Ni sunana Shafiq Kuma naxo ne a madadin malaminku na kira'a, yace in baku hakuri tafiyar gaggawace ta samesa shine ya turoni gashi kuma naga lokaci ya dan kure sabida haka karatu kawai zan kara in yaso in ya dawo duk ku hada haddan ku basa, nan suka bubbude Qur'aninsu ya kara musu karatu cikin muryarsa mai dadin sauraro, kafin ya fita sai da ya sake tunawa Sabbura batun ta zo ta samesa sannan ya fice.




Karfe shabiyu suka tashi Sabbura taja hannun Atika tace muje kawa, Atiqa tace "kiran mallam fa? Sabbura tace " sai dai gobe in na gansa inje amma yau kam sai dai ya hakura dan nasan minti daya na kara anan ina kara wa kaina bala'i ne dan yanzu nasan abunda ke jirana a gida kenan sabida haka muje kawai gwamma hukuncin da zai yanke mun akan bala'in Baba Saude, tabe baki Atika tayi tace "Lalle Sabbura kina hakuri, yaushe zan tsaya matar uba ta mai dani baiwa a gidan ubana, murmushin takaici Sabbura tayi sannan tace " Atika bazaki ganeba iyayena ma basu tsira ba sai ni, dole yasa kika ga nake abunda nakeyi dan gudun magana wa mahaifina, uwata da ta haifeni da ya kamata ita zata na tsayawa  ta karemun hakkina bata damu dani ba toh wat choice do i have, kuma Atika a dane abunda Baba saude ke mun ke damuna amma yanxu na saba ke dai kawai ki dai tayani addu'a, da haka sukayi sallama kowa ya shige gida zuciyan Sabbura cike fal da fargaban abunda zata tarar.

Share:

0 comments:

Post a Comment

Blog Archive

Search This Blog

Contact Form

Name

Email *

Message *