Monday 7 August 2017

RYM 6

🤦🏾‍♀         *Rayuwar*        🤦🏾‍♀

          🙆🏾       *'Ya*    🙆🏾

🙎🏽            *Mace*              🙎🏽

Na B.A. Ladan

♻ *EXCLUSIVE* *WRITERS* *FORUM*

*06*

_Dis page is for ma Admins_
_Maman Ilham_
_Titty luv_
_Hauwa Suleiman (My Kawa)_
_Amiraty( Sista mie)_
_My Luku Luku_&
_My run away Admin Bello Adam Ambursa( please ku tayani cigiyarsa)_
_Kunyi a rayuwa👌🏼, Allah ya barmu tare ya kara dankon zumunci_ *LUSVM*



Xaune take a kofar kitchen nasu tana jira miyanta yayi ta sauke ta raba abinci, Anty Suwaibane ta fito daga dakin Anna cikin daga murya tace "Sabbura baki gama bane? "Saura kadan  Anty, sabbura ta amsa mata " toh kiyi sauri gaskia dan duk yunwa muke ji, Anty suwaiba na gama fadin haka ta koma ciki. 

Cikin nutsuwa ta gama sawa kowa abincinsa a flask ta shigar, a karshe ta dauki na Abbanta tayi sashinsa.

Tun daga bakin kofarsa ta gane yanada baki dan taga takalma. Tsayawa tayi a bakin kofar tayi sallama duk suka amsa mata sannan Abbanta ya mata izini ta shiga, cikin takunta a hankali ta karaso ta aje abincin ta dago dan gaidasu, taga mallam shafiqne da Mal Abakar zuciyanta ba karamin bugawa yayi ba dan duk a tunaninta wani laifin tayi, da kyar ta iya gaishesu ta fice.

Kitchen ta shige ta dauki abincinta ta wuce dakin Anna wajen 'yan'uwanta, tun kan ta karasa take jiyo dariyarsu, da sallamarta ta shiga taga sun juye abincin a kan plate hrda Anna suna ci, gefen kannenta ta zauna inda suma ke cin abincinsu. Har ta gama bata dago ta kallesu ba dan wani zafi da zuciyarta ke mata, hada kayan tayi ta fice dasu sannan ta koma ta dubi kannenta ta ce suje su dau takaddunsu ta musu bitar kratunsu. Da gudu suka fice suna rige-rige, basu jima ba sai gashi sun dawo suka zauna a gabanta ta fara musu karatu suna bi, Anty Saliha ce ta dago tace "a'a baza fa kuma damemu ba, dauki yaran nan kuje can dakin kuyi karatunku, kan ma su tashi Abbanta ya shigo dakin da sallamarsa duk suka juyo tareda amsa mai, kallon Sabbura yayi sannan yace " Kije ana magana dake, kallon juna su anty Suwaiba sukayi suna mamakin wannan abu, Sabbura kuwa bata ma san sunayi ba ta tashi ta wuce dakinsu ta sanya hijabinta ta fito, Abbanta ta gani tsaye a kofarta ya dubeta cikin kulawa yace "kije suna falona, cikin jin kunya ta bi ta gefensa ta wuce.

Cikin tsiririyar muryanta ta musu sallama tareda shiga falon Abbannata, dan nisa da su ta zauna tareda sake gaidasu daga can bata sake cewa komai ba, Mal Abakar ya dubeta yace "Sabbura ga abokina na kawo miki kuma kan muzo sai da muka tunkari Abba kuma ya bamu goyon ba,dafatan kema zaki krbemu hannu bibbiyu dan mu da zafinmu muka zo dafatan zaki krbemu, murmushi tayi tareda sadda kanta kasa tana watsa da yatsunta sannan a hankali tace " Tunda kunyiwa Abba magana kuma ya amince nima na amince, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, "amin suka amsa mata sannan Mallam Abakar ya fita ya basu wuri, hira kadan sukayi sannan suka fito ta rakosa inda Mallam Abakar ke jiransa ta musu saida safe ta koma ciki.

Dakin Anna ta nufa dan duba ko su samira basuyi bacci ba ta karasa musu karatun, hr ta sa hannu zata daga labulen taji Anty Suwaiba na cewa " Anna wa kuma 'yar taki ta samu bamu da labari haka, Allahsa dai baso take ta riga yayyunta aure ba dan mai dunia zatace gamu gardan-gardan a gida ba ko mashinshini a ce ta rigamu
aure.

Shamsiyya ce ta tari numfashinta tace "toh sai me in ta rigamu auren, ai hakan ba haramun bane kuma aure shi nufine na Allah in Allah yace zakayi ko mijin kawarki sai kiga kin aura *(kawa da ke nake🤣)* kuma anan ba yanda Abba baiyi a cire miji ba ku ka ki sabida haka bnga dalili da za ake wannan maganan ba, Anty Suwaiba ta mata wani irin kallo sannan tace " wannan da kike karetan nan ko dai kema auren zakiyi, "in ma zanyi laifine, ko so kike in cigaba da zama har sai kunyi aure, kunda ba niyya yi kuke da ba, dama banso fada yanzu ba amma tunda magana ta taso toh bara inyi kowa yaji, kan mu koma skul iyayen Haidar zasu zo gaisuwa immediately after na gama kuma muyi auren mu, baki bude su Anty Suwaiba ke kallonta sannan ta juyo gun Anna tace " Anna kina jin meh yarinyar nan ke fada, baku san bakin jini zaku shafa mana ba ko, toh wlhy tun wuri ku kau da wannan tunanin dan bazata sabu ba, bakusan illar kanwa ta riga yaya aure bako, bakusan hakan zai iya sawa mu kare rayuwarmu a cikin gidan nan bako, wani yar dariya Shamsiyya tayi tace "Anty Suwaiba wannan duk camfine in kinyi imani da Allah kuma ke mai yarda da kaddarace toh faruwan hakan bazai baki tsoro ba kuma duk abunda zaku ce bazai hanani aurena ba kuma da tuntuni najima da yin auren nan amma na tsaya jiranku amma ynxu kam bnga dalilin da zai sa har sai na jira kunyi aure tukun nayi ba, ganin fadane yake shirin barkewa yasa Anna cewa " Suby rabu da ita, meh abun fada in sun rigaki auren, kr ki manta fadin da ake cewa God saves d best for d last, wani jinkirin alherine sabida haka ki kwantar da hnkalinki besides bn gaji da kallonku ba n ko ba komai zan huta da bakin cikin wannan kanwar taku dan duk sanda na ganta nakanji raina ya baci duniyan duk ta mun baki abun farin cikine a wajena in aka ce zata tafi ta br gidan nan so bn son ki kara tada hnkalinki a kan wannan batu, zama tayi a gefen Anna tareda rungumarta shamsiyya kuwa ta juya ta bar dakin, Sabbura na jin motsin wani na shirin fita ta bar wajen da gudu tayi bayan gidansu inda taje ta takure tana kukarta a hankali, dolene ta nisanta kanta da 'yan uwanta da mahaifiyarta dan wannan tsana da suke mata ya wuce misali, ko bata son Shafiq ta yadda ta aureshi ko dan ta bar gidansu hakan ne kawai zata samu kwanciyar hankali koh ta huta da azabar gidansu, ji tayi an tsunkuya a kanta ta dago ta ga Abbantane sake fashewa tayi da kuka tana "Abba dan Allah kaji tausayina ka kaini gun mahaifiyata dan ban yadda Anna ce ta haifeni ba, Abba ka mun rai ka sadani da mahaifiyata ko sau dayane inji dumin jikinta, inji ya soyayyar uwa yake, kalamanta saida ya sa Abba hawaye ya dubeta yace taso kizo Sabbura

Falonsa suka zauna, sai da yaga ta bar kuka yace " Sabbura banga laifinki dan kin fadi hakan ba amma ki yarda dani in na ce miki Annace mahaifiyarki, bakida wata uwa sai ita Sabbura, "Toh Abba mesa ta tsaneni? ta tambayesa cikin kuka, ajiyar zucia yayi yace " Sabbura bazan iya fada miki dalilin da ya sa mahaifiyarki ta tsaneki ba dan jin hakan zai iya sa kema ki tsaneta ki tsani wanda yayi sanadiyar sa ummarki ta tsaneki, in Allah ya nufa watarana zan fada miki amma a yanxu ba abunda zance dake sai dai ince ki cigaba da hakuri nasan da zafi amma wataran insha Allah zaki ci moriyar hakurin nan taki kuma bnso ki sake dago wannan zancen kinji uwata, kai ta kada sannan yace share hawayenki kije ki kwanta, har ta sa kai zata fice ya sake kiranta ta juyo yace "batun malaminku nayi bincike kuma naga yarone nitsatstse kuma dan gidan mutuncine sabida haka na basa goyon baya amma sauran zabi na gareki amma ina miki kwadayin aurensa dan nasan zai kulamun da ke, murmushi tayi cikin jin kunya tace "Abba nagode sosai, nasan bazaka taba son abunda zai cutardani ba, duk abunda ka aminta da shi nima na aminta da shi, zabinka shine zabina, murmushi yayi dan yaji dadin furucinta yace " Allah miki Albarka Sabbura tashi kije.

Kanta na kasa ta zo ta wuce bata ma lura da Baba Saude da ke zaune ba sai da ta yi tsawa tace "Ke!! zo nan, Sabbura ta juyo cikin tsoro a take jikinta ya hau rawa, durkushewa tayi tana yarfa hannu ganin itacen da ke hannun Baba Saude ta dubeta tace " wato kinyi girman da har zaki na kawo kawaye cikin gidan nan da har zasu ci min mutunci koh,

hada hannayenta tayi waje biyu ta hau bata hakuri tace "Baba Saude kiyi mun rai wlhy wlhy ba sata nayi ba kuma ma tace zata zo ta baki hakuri, dariyar mugunta Baba Saude tayi tace " ba abunda zai hanani jibgarki, wato dama ke a tunaninki wasar tsere da kike mun mantawa nayi da ke, duk taraki nake amma yau watar cin ubanki ya kama,daga itacen tayi zata maka mata ta ji an rike tareda janyewa daga hannunta ta juyo taga Shamsiyya rike da icen tace "ana auran ubanta kuma ake zagin uban nata, ai toh da sai kije kiyi da shi ba ki tsaya kinayi da yar cikinki ba, ynxu ke Baba Saude ko kunya bakiji ki sa yarinya a gaba kiyita jibga, rashin imaninki ma ya wuce misali kuma wlhy bar ganin kina matar ubana ba a taba nawa inyi shiru sai mu kwashi 'yan kallo nida ke a gidan nan, in kuma kince mu gwada toh bismillah, sanin halin shamsiyya sarai zata aikata yasa Baba saude shiga daki tana " ba laifinku bane laifin ubanku ne da ke daure muku gindi.

Karasawa tayi inda Sabbura ke durkushe tana kuka ta dagota sukayi daki.

Har suka shiga dakin Sabbura bata bar kuka ba, da kyar ta rarrasheta tayi shiru, ta dubeta tace "Sabbura ynxu dama zaman da kike a cikin gidan nan knan, bazaki tashi ki tsayawa kanki ba sai ki aje jiki tayi ta jibgarki toh wlhy gwara ki daina dan wannan sakarcine, share kwalla tayi tace " Adda Shamsiyya bazaki taba ganewa ba kawai dai a bar maganan, kuma maganar da kika mata ba wai ta hakura bane, kuna tafiya nasan sai ta huce a kaina shi yasa nake rokonki da duk abunda zata mun dan Allah kr ki mayar mata da magana ko ba komai matsayin uwa take a wajenmu musayar yawu da ita rainini bazan so kuma a dalilina kike hakan ba har azo ana fushi dake sabida haka pls ina rokonki ki bari, tana gama fadin haka ta dauki sallaya da hijabinta ta fice dan bata so maganar yayi nisa.




♨♨♨♨♨♨♨♨

Cikin shiri Rufaida ta sauko sai kamshi take, falon Abbansu ta shige inda ta tarar da shi yana karanta jarida ta zo ta zauna gefensa tareda gaishesa, ya dubeta cikin zolaya yace "amarya a gidan shureim irin wannan kyau haka, daria tayi tace " Daddy bnda zolaya dai, yace "ai ma princess ko ynxu aka je gasar miss world ba ko shakka ke zaki ci dan duk dunia dia isn't any one as beutiful as u bt dts besides ur mum ya fada cikin alamun da ya nuna ya ji zafin maganar, saukar da knta kasa tayi dan tasan duk lokacin da aka ambaceta duk suna shiga wani yanayi, dagowa tayi tace " Abba dama wata magana naxo muyi, gyara zamansa yayi yace "ina jinki princess, " dama a kan Nani ne, sai kuma tayi shiru, Daddy yace go on princess, a hankali tace "Abba me zai hana ka auri Nani, zamanku haka a gidan nan bn jin dadi n shs bn wt us tun da muka dawo Nigeria kuma duk kowa ya yaba da halinta, shs gonna b a perfect wife to u n a mum to us kuma na san in na tafi zata tayani kulawa daku, ajiyan zucia Daddy yayi sannan yace " Nagode princess da kulawarki garemu nida lil bro inki, bawai banki shawararki ba but i will think about it kafun ki tafi zaki ji amsa na, dan hugging nasa tayi tace " i hope to hear a positive answer bari in shiga hau in duba dan rikicin tun jiya ya kulle kansa a daki, dariya daddy yayi yace "kunfi kusa shi yasa bn shiga ba kr anjima inji kunya, dariya itama tayi sannan ta haura sama.

Ganin baya daki ya sa ta sauko ta shige dakin Nani ta tarar tana sallah zama tayi ta idar ta juyo tace " Nani shigowa nayi in tambayi dan wajen naki dan tun jiya yake fushi dani, murmushi tayi sannan tace "Rufaida ashe dama ke ki tabo mun shi, toh maza kije kiyi biko, yana can dakin da ke gaban gida dan in abu ya damesa can yake zuwa yayi zamansa, tashi Rufaida tayi tace " Nanj barinje toh, wannan dan naki sai ku gwara ma inyi in tafi in barku ku karata sannan ta fice.

Kai tsaye ta shiga dakin bako sallama, mutuwar tsaye tayi a bisa abunda ta gani cikin daga murya tace MK what the f...................!


♻ *Billy Ladan* ♻

Share:

0 comments:

Post a Comment

Blog Archive

Search This Blog

Contact Form

Name

Email *

Message *